Sheikh Dahiru Bauchi Yayi Suka Kan Maganar Haramta Almajirci

0 117

Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gargadi gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihoshi dangane da haramta tsarin karatun Almajiranci.

Malamin ya ayyana cewa Almajirai suna da ‘yancin gudanar da addininsu ba tare da wata tsangwama ba a kudin tsarin mulki.

Da yake jawabi a karshen taron ganawar malaman Tsangaya, Sheikh Dahiru Bauchi ya bukaci a kyale Almajirai su cigaba da karatunsu na Al’Qur’ani a karkashin malamansu.

A cewarsa, hakane ya kamata saboda Almajirai kamar kowane  dan Najeriya, suna da damar gudanar da addininsu da yancin zama duk inda suka ga dama a cikin kasa, kamar yadda aka tabbatar a kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Ya ayyana cewa malaman Tsangaya baza su lamunci a take musu hakki ba ta hanyar haramta tsarin Almajiranci, da kuma kwashe Almajirai daga gari zuwa wani gari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: