Wani matashi ya cinna wa masallaci wuta ana tsaka da Ibada

0 310

‘yan sandan Kano ta ce tana ci gaba da bincike kan lamarin wanda ya faru a Gabasawa, sannan za ta yi ƙarin bayani kan lamarin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta yayin da mutane ke Sallar Asuba yau Laraba.

Lamarin ya faru ne a garin Larabar Abasawa da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a jihar ta Kano.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa da faruwar lamarin da kama mutumin da ake zargi, sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Rahoatanni sun ce an garzaya da mutanen da suka jikkata sakamakon faruwar lamarin asibiti, inda suke karɓar magani, sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani kan ko an samu asarar rayuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: