

Rundunar yansanda ta jihar Jigawa ta kama wasu matasa da ake zargin sun kware wajen satar babura a sakatariyar gwamnatin jiha dake Dutse.
A wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdu Jinjiri ya bayar, ta bayyana sunan mutanen da suka hada da Najib Salisu mazaunin Tarauni a Kano da Yusif Ibrahim mazaunin Dala a Kano da kuma Musa Nasiru dake zaune a Tudun Wada, Kaduna.
- Kungiyar likitoci sun janye yajin aiki sun bada sati hudu
- Hadejia: Za’a kaddamar da filin wasan kwallon doki da tsere a Hadejia (Polo club and race course).
- Zidane: Kasancewar Messi a Spain na karawa gasar La Liga daraja
- Majalisar wakilan Najeriya na duba yiwuwar tilasta bai wa mata sojoji damar sanya hijabi
- Yarima Philip Mijin Sarauniyar Ingila Ya Mutu
Mutanen uku da aka kama wadanda suke dauke da makulli na musamman da barayi ke anfani dashi wajen bude ababan hawa, sun ce suna satar babura daga wannan jiha zuwa wata, sannan kuma su sayar da baburan a kasuwanni.
Sanarwar ta kara da cewa mutanen 3n sun kuma tabbatar da cewa suna kokarin satar babur a sakatariyar gwamnatin jiha dake Dutse lokacin da aka kama su.
Yansanda na cigaba da gudanar da bincike dangane da lamarin.