

Gwamnatin tarayya ta amince da dawo da jigilar jiragen sama a cikin kasa da zarar komai ya daidaita, bisa tanadin ka’idojin kariya daga cutar corona na cikin gida da na kasa da kasa.
Shugaban kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona, Boss Mustapha, ya sanar da haka wajen taron manema labarai na kwamitin a Abuja.
Yace dawowa jigilar jiragen zata zo da karin kudin tikitin jirgin sama.
- Tarihin Gamuwa 10 Tsakanin Kano Pillars VS Eyimba Da Kuma Wasan Yau
- Abubuwa 5 da suka zama wajibi lokacin sanyi
- An ƙaddamar da kudin kariya ga ƴan jarida da masu fafutukar ƴancin amfani da yanar gizo
- Yadda ake duba suna don zama ma’aikacin damara na 2020 a Nijeria
- Me Ƙungiyar Izala ta ce kan matsalolin tsaro a Najeriya?
Yayi bayanin cewa karin kudin kayayyaki da na ayyuka, ba bangaren sufurin jiragen sama kadai ya shafa ba.
A cewarsa, farashin abubuwa sun yi tashin gwauron zabi tun bayan barkewar annobar.
An rufe filayen jiragen sama a Najeriya a watan Maris, lokacin da kasar ta fara kokarin dakile bazuwar cutar corona, wacce tayi silar mutuwar sama da mutane 500 a kasarnan.