

Ministan aikin gona da raya karkara, Sabo Nanono, yace gwamnatin tarayya ta ware kudi naira biliyan 600 domin inganta baiwa manoma damar samun lamunin kudaden aikin gona a kasarnan.
Sabo Nanono yace kimanin manoma miliyan 2 da dubu 400 ake sa ran zasu amfana daga bashin wanda babu kudin ruwa a ciki, da aka tsara da nufin kara karfin gwiwar amfani da fasahar zamani wajen noman shinkafa da sauran amfanin gonar da ake sayarwa.
- Za A Yi Kididdigar Masu Aikin Karuwanci A Bauchi
- Kuji tsoron Allah ko koma gare Shi, Atiku yayi kira ga yan Najeriya.
- Goodluck Jonathan: Kuri’un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba
- Sarkin musulmi: Gobe Talata shine daya ga watan Ramadan
- Kamfanin Twitter zai kafa reshe a Afirka
Ministan yayi jawabi a wajen kaddamar da shirin tallafawa noman shinkafa na daminar bana a kauyen Tofai dake yankin karamar hukumar Gabasawa ta jihar Kano.
Sabo Nanono yace shirin zai agazawa manoma wajen samun nasarar habaka yawan amfanin gona, da dogaro da kai da kuma yalwar abinci a kasa.