2027: Yau INEC Za Ta Yanke Hukunci Kan Makomar Pantami, Gwarzo, Adebutu da Wasu

0 13

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), na shirin yanke hukunci kan ko za ta saka sunayen wasu ’yan takarar gwamna cikin jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027.

Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Isa Ali Pantami na Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe, Abdulsalam Gwarzo na NDC a Kano, da Ladi Adebutu na jam’iyyar PDP a Jihar Ogun.

INEC ta cire sunayensu daga cikin jerin da ta fitar a watan Oktoba, tana mai cewa wasu jam’iyyun siyasa ba su gabatar da rajistar mambobinsu kamar yadda doka ta tanada ba.

Ana sa ran hukumar za ta duba ƙorafe-ƙorafen da ’yan takarar da jam’iyyunsu suka shigar kafin yanke hukunci kan lamarin.

Gwarzo ya maka INEC a kotu, inda yake neman kotun ta bayyana cire sunansa a matsayin haramtacce.

Ya kuma nemi kotun ta umarci hukumar ta amince da shi da mataimakinsa a matsayin ’yan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC.

Haka kuma, Adebutu ya nuna rashin amincewarsa kan cire sunansa, yana mai cewa har yanzu shi cikakken mamba ne na PDP kuma ya gabatar da takardun da ake buƙata cikin wa’adin da aka ƙayyade.

A halin da ake ciki, wasu magoya bayan Pantami a Jihar Gombe sun gudanar da addu’o’i domin neman nasarar burinsa na zama gwamna.

Farfesa Atah Pine, masanin harkokin siyasa, ya ce ’yan takarar da abin ya shafa za su iya neman haƙƙinsu a kotu idan INEC ta ƙi mayar da sunayensu cikin jerin ’yan takarar.

Ana sa ran hukuncin hukumar zai fayyace ko waɗannan ’yan takara za su samu damar fafatawa a zaɓen gwamna na 2027.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner