Jam’iyyar ADC ta ɗage ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Jihar Sakkwato daga ranar 31 ga watan Oktoba, zuwa ranar 4 ga watan Nuwamba, 2026.
Daraktan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a Jihar Sakkwato, Bello Aliyu Goronyo ne, ya sanar da sauya ranar cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Goronyo, ya ce an ɗauki matakin ne domin magance wasu matsalolin shirye-shirye da daidaita ayyuka, don tabbatar da gudanar da taron cikin nasara.
Ya bayar da haƙuri kan duk wata matsala da sauya ranar zai iya janyo, tare da gode wa shugabannin jam’iyyar, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki bisa fahimtarsu da goyon bayansu.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen ya buƙaci duk waɗanda abin ya shafa su lura da sabuwar ranar da aka sanya.
Sannan ya ce yana fatan tarbar shugabannin jam’iyyar, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki a wajen taron.