Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ta ce tana shirin kafa asusun tallafin karatu naira biliyan ɗaya a shekara mai zuwa, domin tallafa wa ɗaliban jami’ar da ba su da hali.
Shugaban ƙungiyar na duniya, Baba Shettima Kukawa, ne ya bayyana hakan yayin taron shekara-shekara na ƙungiyar a Abuja.
Ya ce tallafin zai haɗa da kuɗin karatu da na gudanar da rayuwar yau da kullum, yayin da za a tantance adadin waɗanda za su amfana bisa kuɗin da aka samu da kuma buƙatunsu.
Kukawa ya kuma bayyana cewa ƙungiyar na shirin kafa kwamitin bunƙasa ƙwarewar sana’o’i a fannoni biyar, ciki har da lissafi, shari’a, likitanci da ilimin ƙasa, domin ƙarfafa jagoranci da musayar ilimi tsakanin tsofaffi da sababbin ɗalibai.
Ya ce kusan tsofaffin ɗalibai 10,000 ne suka yi rajista ta shafin intanet ɗin ƙungiyar cikin watanni huɗu.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammed Laminu Mele, ya buƙaci tsofaffin ɗaliban da su ƙara tallafa wa ci gaban jami’ar da kuma dorewar ƙwarewa a fannin ilimi.
Ya ce gudunmawarsu na da muhimmanci wajen bunƙasa jami’ar da ci gaban ƙasa.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Jami’ar Legas ta duniya, Injiniya Ifeoluwa Oyedele, ya yaba da juriyar jami’ar wajen ci gaba da gudanar da ayyukanta duk da matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa maso Gabas.
Ya kuma buƙaci ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai su samar da shirye-shiryen jagoranci da taimaka wa matasa wajen fuskantar ƙalubalen rashin aikin yi da sauran matsalolin rayuwa.