Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya buƙaci magoya bayansa da su ƙara ƙaimi, yana mai cewa har yanzu yana nan daram a takarar Shugaban ƙasa ta 2027, kuma babu wata barazana da za ta sa ya janye.
Atiku ya bayyana hakan ne bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin ADC ƙarƙashin Sanata David Mark tare da rushe duk matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa ranar Juma’a, Atiku ya ce babu wata barazana, cin zarafi ko dabarar shari’a da za ta sa ya bar takarar ko ya yi watsi da magoya bayansa.
Ya kuma yi zargin cewa, hukuncin kotun bai yi daidai da muradin ’yan Najeriya ba, yana mai cewa ya kamata a bar al’umma su zaɓi wanda suke so.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya zargi jam’iyyar da ke mulki da amfani da matsin lamba na siyasa da wasu dabaru domin raunana ’yan adawa, maimakon ta gabatar da ayyukanta ga ’yan Najeriya.
Ya kuma yi zargin cewa, ana ƙoƙarin amfani da hotunan da AI ta ƙirƙira da bayanan bogi wajen gurɓata rajistar masu zaɓe.
Atiku ya kuma soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kan cire tallafin man fetur ba tare da tanadin kariya ga ’yan ƙasa ba, faɗuwar darajar Naira da tsadar abinci. Ya ce, dole ne a kare dimokuraɗiyya tare da bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar fafatawa cikin adalci a zaɓen 2027.