Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa tana sane da ƙorafe-ƙorafen da ake yi kan tsadar rayuwa, amma tana ƙoƙarin shawo kan matsalolin tattalin arzikin ƙasar.
Shettima ya bayyana hakan ne ranar Litinin a birnin Kalaba na Jihar Kuros Riba, lokacin da yake jawabi ga al’ummar yankin Kudu maso Kudu da sauran ’yan Najeriya a wani taron yaƙin neman zaɓen Tinubu da Gwamna Bassey Otu.
Ya ce gyaran tattalin arziki ba abu ne da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa ba, amma duk da ƙalubalen da ake fuskanta, gwamnatin Tinubu na yin iya ƙoƙarinta, kuma ana samun ci gaba a fannin tattalin arziki.
Mataimakin shugaban ƙasar ya buga misali da ƙasar Singapore, wadda ya ce ta sha fama da matsalolin tattalin arziki, amma ta samu ci gaba bayan al’ummarta sun yi haƙuri da ba gwamnati goyon baya da haɗin kai.
Ya ce gwamnatin Tinubu na neman irin wannan haƙuri da goyon baya daga ’yan Najeriya domin samun damar ci gaba da ayyukan raya ƙasa.
“Don haka wannan gwamnati ta Bola Ahmed Tinubu tana neman ku ƙara haƙuri da juriya, tare da ba ta goyon baya ta hanyar zaɓen ta a shekarar 2027 domin ci gaba da ayyukan raya ƙasa,” in ji shi.
Shettima ya ƙara da cewa gwamnati ta fara ayyukan raya ƙasa a yankin Kudu maso Kudu, tun daga Kuros Riba zuwa Akwa Ibom da Delta, sannan ta nufi jihohin Kudu maso Yamma.
Ya ce idan ’yan Najeriya suka sake zaɓen gwamnatin Tinubu, za ta faɗaɗa ayyukan raya ƙasa a sauran sassan ƙasar.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kuros Riba, Sanata Bassey Otu, ya ce jam’iyyar APC ba ta samu nasara a dukkan ƙananan hukumomin jihar ba a zaɓen da ya gabata.
Ya ce daga cikin ƙananan hukumomi 18 na jihar, APC ta samu nasara a bakwai kacal, amma a zaɓen 2027 suna fatan lashe dukkan ƙananan hukumomin.
“Ku sani fa, a zaɓen 2027 za mu yi 18 bisa 18, wato APC za ta lashe dukkan ƙananan hukumomi 18 na jihar nan, tun daga sama har ƙasa,” in ji gwamnan.
Shi ma Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Tinubu da Bassey Otu a ƙarƙashin ƙungiyar Hausawa da Fulani, Alhaji Nasiru Baba Gombe, ya sha alwashin cewa al’ummar Hausawa da Fulani da ke jihar za su mara wa APC baya a zaɓen.
Ya ce suna da niyyar ganin dukkan ’yan takarar jam’iyyar sun yi nasara, daga matakin sama har ƙasa.
Ya kuma yi iƙirarin cewa jam’iyyun adawa ba za su samu gagarumar nasara a jihar ba, inda ya ce APC ce za ta yi nasara a zaɓen.