Amurka Ta Kai Hare-Hare Kan Tsibirin Qeshm Na Iran

0 11

Amurka ta kai hare-hare kan tsibirin Qeshm na Iran a ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito, tana mai ambaton wasu jami’an gwamnatin Amurka.

Rahoton ya ce an kai hare-haren ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ke ƙoƙarin rage fargabar sake ɓarkewar babban rikici tsakanin ƙasashen biyu, yayin da ake shirin gudanar da zaɓen tsakiyar wa’adi na Majalisar Dokokin Amurka.

Wani jami’in Amurka ya bayyana hare-haren a matsayin matakin kariya, saboda Iran ta yi amfani da makamai masu linzami wajen kai hare-hare kan kadarorin Amurka.

A cewar jami’an Amurkan da jaridar ta ambata, sojojin ƙasar sun ci gaba da kai ƙananan hare-hare kan wasu wuraren Iran tsawon makonni.

Sun ce an kai hare-haren ne domin hana Iran samun ƙarfin da zai ba ta damar yin barazana ko kai hari kan jiragen kasuwanci da ke wucewa ta Mashigar Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga zirga-zirgar jiragen ruwa da cinikayyar duniya.

A safiyar Talata kuma, an ji ƙarar fashe-fashe a kudancin Iran, ciki har da tsibirin Qeshm da birnin Bandar Lengeh da ke gaɓar teku, a cewar rahotannin da kamfanonin dillancin labaran ƙasar suka fitar.

Trump ya ce ba zai sake kai hari ba
A ranar Litinin, Trump ya yi watsi da yiwuwar sake kai hare-haren soji kan Iran bayan zaɓen tsakiyar wa’adin inda ya jaddada cewa ƙoƙarin diflomasiyya na samun ci gaba.

Da wani ɗan jarida ya tambaye shi ko yana shirin sake kai hari kan Iran bayan zaɓen, Trump ya amsa da cewa, “A’a.”

Sai dai shugaban Amurkan ya jaddada cewa ba zai taɓa bari Iran ta mallaki makaman nukiliya ba, ya kuma nanata cewa jami’an ƙasar sun fahimci matsayar Amurka kan wannan batu.

Ya ce hana Tehran mallakar makaman nukiliya na da matuƙar muhimmanci, inda ya yi gargaɗin cewa Iran ba za ta iya ci gaba da gudanar da al’amuranta kamar yadda take yi a yanzu ba idan ta samu irin wannan ƙarfin.

“Mun dakatar da hakan a shekarar da ta wuce ta hanyar amfani da manyan jiragen yaƙinmu samfurin B-2, waɗanda suka kai hari kan dukkan wuraren, suka binne komai a ƙarƙashin ɗaruruwan tan na duwatsu,” in ji Trump.

Ya kuma bayyana cewa tattaunawar diflomasiyya na tafiya yadda ya kamata, yana mai danganta yiwuwar cimma yarjejeniya da raguwar farashin makamashi.

“Wataƙila hakan ne ya sa farashin mai ya faɗi sosai,” in ji shi.

Tun da farko, Trump ya shaida wa manema labarai cewa, “Mun yi yaƙi da Iran. Mun yi nasara.”

Sai dai ya ƙara da cewa bai ma san ko za a iya kiran abin da ya faru da yaƙi ba, domin Amurka da Iran ba su fafata ba tsawon watanni.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner