Gwamnatin Jihar Sakkwato ta rufe ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC da ke ginin Savannah Bank, a kan titin Ahmadu Bello da ke cikin birnin Sakkwato.
Kwamishinan Filaye da Gidaje na jihar, Barista Nasir Aliyu Dantsoho, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, lokacin da ya kai ziyara ofishin tare da tawagarsa.
Ya ce gwamnati ta yanke shawarar rufe ofishin har sai abin da hali ya yi, bayan abin da ta bayyana da cewa ta gaza samun cikakken bayanai kan mallakar ginin.
Kwamishinan ya bayyana cewa sun rubuta wa hukumar da ke kula da ginin domin neman bayani kan matsayinsa na mallaka, amma har yanzu ba su samu wani martani ba.
Ya ce za a ci gaba da rufe wurin har sai gwamnati ta samu bayanan da take nema ko kuma mai mallakar ginin ya gabatar da takardun shaidar mallaka domin tantancewa.
“Duk wanda ya saɓa wa wannan umarni na gwamnati ta hanyar shiga gidan ko yin wata mu’amala a cikinsa zai fuskanci shari’a bisa laifin da ya aikata,” in ji kwamishinan.
Ya ƙara da cewa ginin zai ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon gwamnatin jihar har sai an warware batun mallakarsa ko kuma mai shi ya gabatar da takardun shaidar mallaka domin tantancewa.
Dantsoho ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin shiga wurin da aka rufe da ƙarfi zai fuskanci matakin shari’a, ciki har da gurfanar da shi a gaban kotu.
Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi a Sakkwato, sakamakon zarge-zargen hare-hare da suka shafi magoya bayan ADC da jami’an wata rundunar tsaro mallakar gwamnatin jihar.