Sultan Ginshikin Hadin Kai da Zaman Lafiya Ne – Gwamna Lawal

0 11

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a matsayin jagoran da ke karfafa hadin kai da zaman lafiya, wanda shugabancinsa ke karfafa gwiwar ’yan Najeriya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Litinin a taron makon Sheikh Usmanu Dan Fodiyo karo na 13, da kuma bikin cika shekaru 20 da nadin Sarkin Musulmi a matsayin sarki, wanda aka gudanar a cibiyar taro ta kasa da kasa da ke Sakkwato.

Taken taron shi ne, “Farfaɗo da shugabanci nagari da zaman lafiya a cikin al’umma: Darussan da za a koya daga shugabannin jihadin Sakkwato”.

A sakon taya murna, Gwamna Lawal ya ce hikima da shawarwari da shugabancin Sarkin Musulmi na ci gaba da karfafa gwiwar gwamnatin Zamfara da al’ummarta, musamman a lokutan kalubalen rashin tsaro da matsalolin zamantakewa.

Ya taya Sarkin Musulmi murna a madadin al’ummar Zamfara, yana mai bayyana cika shekaru 20 a kan karagar mulki a matsayin wani muhimmin tarihi.

Gwamnan ya kuma gode masa bisa halartar bikin nadin sarautar gargajiya da mika sandunan mulki ga sarakuna 19 na jihar Zamfara a Gusau, yana mai cewa hakan na nuna yadda yake kokarin karfafa cibiyoyin sarautun gargajiya a yankin.

Ya ce darussan da aka gada daga daular Usmaniyya sun hada da neman ilimi, adalci, kyawawan dabi’u, shugabanci nagari da mutunta dan Adam.

Gwamna Lawal ya kara da cewa jihar Zamfara na da dalilan yin koyi da koyarwar Sheikh Usmanu Dan Fodiyo, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar matsalolin rashin tsaro, talauci, tabarbarewar dabi’u da kuma barazanar da ke addabar matasa.

A nasa jawabin, Sarkin Musulmi ya gode wa daidaikun mutane da kungiyoyin da suka mara masa baya a tsawon shekaru 20 na mulkinsa.

Ya kuma bukaci shugabannin addini, sarakuna da na al’umma da su kara kokarin tabbatar da zaman lafiya da dankon zumunci a tsakanin jama’a.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner