Amirul Hajj Alhaji Najib Husssain Adamu ya kai ziyara masaukan maniyatan jihar Jigawa dake birnin Madina
Amirul Hajj na jihar Jigawa kuma mai martaba sarkin Kazaure Alhaji Najib Husssain Adamu ya kai ziyara masaukan maniyatan jihar Jigawa dake birnin Madina.
Mai martaba sarkin wanda ya taya su murna samun damar zuwa kasa mai tsarki domin gabatar da aikin hajjin bana, ya nuna gamsuwa da halayyar maniyatan tare da fatan kiyayewa da dokoki da kaidojin kasa mai tsarki.
Alhaji Najib Hussain Adamu ya kuma koka musu bisa yadda wasu maniyatan aka so yi musu zamba cikin aminci wajen sanya hakori da kuma chanjin kudi.
Maniyatan sun kokowa Amirul Hajj na samun tseiko wajen shiga Rauda , inda ya ce bisa tsarin Saudia a bana sai an aikewa da maniyaci sako ta kafar sadarwa ta zamani sannan zai shiga cikin Rauda.
Ya bukace su dasu kasance masu hakuri da kuma juriya.
A nasa jawabin Darakta janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar labbo ya nuna jin dadinsa bisa wannan ziyara tare da bayyana amirul hajj a matsayin jagora na kwarai abin misali.
Kakakin hukumar alhazan na jiha Habibu Yarima ya ce amirul hajj ya samu rakiyar tawagar sa da kuma jamian hukumar alhazai ta jiha.