Gwamnan Kano ya yi wa malaman jami’o’i ƙarin albashi
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da ƙarin albashi ga malaman jami’o’in jihar da sauran ma’aikatansu.
Ƙarin albashin zai shafi Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil da Jami’ar Northwest.
Gwamnan ya amince da ƙarin ne bayan wani kwamiti da Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta kafa ya duba buƙatar jami’o’in biyu ta mayar da sabon tsarin albashin cikin tsarin jihar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin, sabon tsarin albashin ya fara aiki daga watan Janairun 2026, yayin da za a fara biyan ƙarin daga watan Satumba.
Sanarwar ta ce la’akari da ƙarin albashin ma’aikatan jami’o’in biyu gwamnatin jihar za ta kashe kusan Naira miliyan 391.8 a kowane wata, wanda ya haura Naira biliyan 4.7 a shekara.
Ta ce matakin ya biyo bayan sabon tsarin albashin da Gwamnatin Tarayya ta fara amfani da shi a jami’o’in tarayya.