Gwamnatin Jigawa Ta Kayyade N7.67m Kuɗin Hajjin 2027

0 31

Gwamnatin Jigawa ta ƙayyade N7.67m kuɗin Hajjin 2027

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙayyade Naira miliyan 7,672,822a matsayin kuɗin aikin kujerar Hajji na shekarar 2027.

Daraktan-Janar na hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya fitar.

Ya ce alhazan da suka riga suka biya kuɗin farko na Naira miliyan 7.5, yanzu za su ƙara biyan Naira 172,822 domin cika sauran kuɗin aikin Hajjin.

Alhaji Labbo ya ce 18 ga Satumba, 2026 ce ranar ƙarshe da aka sanya wa maniyyatan jihar domin kammala biyan kuɗin.

Ya kuma umarci jami’an hukumar da ke yankuna daban-daban da su ƙara kaimi wajen wayar da kan alhazai, tare da tabbatar da cewa sun kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace.

Daraktan-Janar ɗin ya yaba wa jami’an hukumar bisa haɗin kai da ƙoƙarin da suke yi wajen tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin.

Ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, bisa tallafin da yake bai wa hukumar wajen gudanar da aikin Hajji, musamman samar da lamuni da ke taimaka wa alhazai wajen samun kujerun aikin Hajjin.

Hukumar ta buƙaci dukkan alhazai da abin ya shafa da su gaggauta biyan sauran kuɗin kafin cikar wa’adin da aka sanya, domin kauce wa tsaiko a shirye-shiryen tafiyar aikin Hajjin.

Leave a Reply