Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta samar ma ta da sabuwar mota da kuma babur masu kafa uku domin inganta aikin tattara shara a fadin jihar.
Manajan Darakta na hukumar, Malam Adamu Sabo, ne ya bayyana hakan yayin wani shiri a gidan rediyon Jigawa da aka gabatar domin bikin cikar Gwamna Umar Namadi shekaru biyu a kan karagar mulki.
Malam Adamu Sabo ya bayyana cewa hukumar ta gina wurin zubar da shara guda 12 a bara, kuma tana ci gaba da aikin gina wadanda suka kai 20 a halin yanzu a sassa daban-daban na jihar.
Ya kara da cewa hukumar ta gudanar da aikin share magudanan ruwa da feshin maganin sauro a wasu kananan hukumomi domin dakile yaduwar cututtuka.
Haka kuma, ya ce an fara gina wuraren zubar da shara a manyan asibitoci uku da ke jihar domin saukaka tsafta a cibiyoyin kiwon lafiya.
A cewarsa, an mayar da aikin tsaftar muhalli na wata-wata, domin kara tabbatar da tsafta a cikin al’ummar jihar.
Kazalika, hukumar ta kaddamar da sabon shirin sarrafa sharar gida domin amfanin al’umma da kare lafiyar muhalli.