Gwamnatin tarayya ta ce tsare-tsaren da sauye-sauyenta sun yi nisa kan harkokin karyar da farashin kayayyakin abinci da zimmar tabbatar da wadatar kasa da abinci, sauki da rahusa kuma al’ummar kasar na samu ta kowani bangare.
Ministan albarkatun noma da wadata kasa da abinci, Sanata Abubakar Kyari, shi ne ya shaida hakan a hirarsa da ‘yan jarida a Maiduguri.
Kyari ya bayyana himmar da gwamnati ke ci gaba da yi a bangaren noma domin ta dakile matsalar karancin abinci da kuma farfado da tattalin arziki.
Ya ce ma’aikatarsa ta yi amfani da dabaru daban-daban domin tunkarar kalubale kamar rashin tsaro, ambaliya, da dogaro da shigo da kayayyaki, musamman a wuraren da ke da matukar muhimmanci kamar noman alkama da shinkafa.
A wani bangare na kokarin rage sama da tan miliyan shida na alkama da ake shigowa da su duk shekara, yace sun kaddamar da shirin noman alkama na kasa.
Ya kuma ce Nijeriya ta yi hadin gwiwa da kasar Belarus don samar da ayyukan hadaka da nufin kara yawan kayan da ake fitarwa.
Ministan ya yi gargadin cewa a guji amfani da injinan noma da gwamnati ta samar ba ta hanyoyin da suka dace ba, inda ya bukaci manoma da su yi amfani da irin wadannan kayan aikin yadda ya kamata.