Gwamnatin Tarayya Ta Samo Tallafin Dala Miliyan 300 Daga Bankin Duniya Domin Taimakawa Yan Gudun Hijira a Arewa

0 402

Bankin Duniya ya amince da bayar da tallafin kuɗi na dala miliyan 300 ga Najeriya domin ƙarfafawa ‘yan gudun hijira (IDPs) da al’ummomin da suke zaune tare da su a Arewacin ƙasar. Wannan amincewa, wadda aka tabbatar a ranar 7 ga Agusta, 2025, za ta tallafa wa Shirin Magance Matsalolin ‘Yan Gudun Hijira da Al’ummomin da Suke Kula da Su “Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project (SOLID), wanda zai mayar da hankali kan wasu ƙananan hukumomi da rikice-rikicen tsaro suka fi addaba.Ana sa ran shirin SOLID zai amfanar da mutum sama da miliyan 7.4, ciki har da ‘yan gudun hijira miliyan 1.3, ta hanyar amfani da tsari mai ɗorewa da ya dace da ci gaban Najeriya.

Bankin ya ce rikice-rikice da rashin tsaro a yankin sun raba fiye da mutane miliyan 3.5 da muhallansu, lamarin da ya kawo matsanancin matsin lamba kan ababen more rayuwa da hidimomin da ke yankunan da ‘yan gudun hijira suka fakewa.Shirin zai dora ne kan ayyukan da gwamnati ke yi yanzu, tare da haɗa gudunmawar da ƙasashen duniya ke yi, domin farfaɗo da yankunan da rikice-rikice suka shafa a gajeren lokaci.

Leave a Reply