Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam irin su Human Rights Writers Association of Nigeria (HURIWA) sun gargaɗi ‘yan sanda da su guji amfani da karfi wajen fatattakar masu zanga-zangar lumana.
HURIWA, ta bakin babban jami’inta Emmanuel Onwubiko, ta bayyana damuwa kan yadda a baya jami’an tsaro suka yi amfani da makamai wajen tarwatsa masu zanga-zanga, wanda hakan ya janyo rasa rayuka da samun raunuka.
Ta bukaci babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun da ya tabbatar da cewa jami’ansa ba za su yi amfani da makamai ba kan masu zanga-zangar gobe Alhamis.
A cewarta, ‘yancin fadar albarkacin baki da taro cikin lumana, wata doka ce ta tsarin mulkin Najeriya, ba izinin gwamnati ba ce.