Kashi 40 Cikin 100 Ne Na Asibitoci Suke da Tsabta A Duniya – MDD

0 29

Kashi 40 cikin 100 ne na asibitoci suka da tsabta – MDD

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce kashi 40 cikin 100 ne kawai na cibiyoyin kiwon lafiya a duniya ke da banɗakuna masu tsabta da sauran muhimman kayayyakin tsafta da suka dace da marasa lafiya da ma’aikatan lafiya.

A cikin wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da UNICEF suka fitar, an nuna cewa kashi 11 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya ba su da wata hidimar tsafta kwata-kwata, lamarin da ke shafar kusan mutum miliyan 936 a faɗin duniya.

Rahoton ya kuma bayyana cewa akwai babban bambanci tsakanin yankuna, inda kashi 23 cikin 100 ne kawai na asibitocin da ke yankin Afirka ta kudu da Sahara ke da ingantattun ayyukan tsafta, idan aka kwatanta da kashi 55 cikin 100 a yankunan Tsakiya da Kudancin Asiya.

Baya ga tsafta, rahoton ya ce kashi 85 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya suna da wadataccen ruwa, amma ƙasa da kashi 60 cikin 100 ne suka cika ƙa’idojin tsaftace muhalli da hana yaɗuwar cututtuka, musamman a ƙasashe masu ƙarancin ci gaba

Leave a Reply