Kotu Ta Yanke Wa Sojoji 66 Hukuncin Kisa A Kongo

0 31

Wata kotun soji a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ta yanke wa dakaru 66 hukuncin kisa bayan ta same su da laifin tayar da ƙayar baya, ƙin bin umarnin shugabanni da kuma ja da baya a fagen daga.

Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun rawaito cewa an gudanar da shari’ar a Kotun Sojoji da ke yankin Goma a lardin Arewacin Kivu, inda aka gurfanar da sojoji sama da 70.

Gidan rediyon Majalisar Ɗinkin Duniya, Radio Okapi, ya ruwaito cewa kotun ta wanke sojoji huɗu daga zarge-zargen da ake musu, yayin da ta yanke wa wani ɗaya hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari.

Rahoton ya ce sojojin da aka samu da laifin na cikin runduna ta 3415 ta sojojin ƙasar, kuma an kama su ne a ranar 20 ga Oktoba a yankin Walikale, inda ake zargin sun aikata laifukan.

Rundunar sojin ƙasar ta ce ɗaya daga cikin dalilan gudanar da shari’ar shi ne ƙarfafa ladabtarwa da bin ƙa’ida a cikin rundunar, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar matsalar tsaro a gabashin ƙasar.

A watan Oktoba, wata kotun soji a ƙasar ta yanke wa wasu sojoji 27 hukuncin kisa bisa zargin nuna tsoro bayan sun tsere daga filin daga yayin yaƙi da ’yan tawayen AFC/M23.

Hukuncin na baya-bayan nan ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da gwabza faɗace-faɗace a gabashin Congo tsakanin dakarun gwamnatin ƙasar da ƙungiyar ’yan tawaye ta AFC/M23, wadda ke ƙoƙarin faɗaɗa ikonta a yankin.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner