Kwastam Ta Kama Mutum 2 Kan Fasaƙwaurin Bindigogi 399

0 49

Kwastam ta kama mutum 2 kan fasaƙwaurin bindigogi 399

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama wani mai shigo da kaya daga ƙasashen waje da wata mata mai fiton kaya bisa zargin shigo da bindigogi 399 ba bisa ka’ida ba, ta tashar Tin Can Island da ke Legas.

Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce an gano bindigogi ƙirar Jojef pump-action guda 399 ne a cikin wani kwantaina da ta iso tashar a ranar 8 ga Yuli.

Ya bayyana cewa masu fasaƙwaurin sun kwakkwance bindigogin tare da ɓoye su a cikin kwantainar domin kauce wa binciken jami’an tsaro.

Ya ƙara da cewa bayan da aka sake haɗa makaman, jami’an Kwastam sun samu bindigogi 399 da kuma sassan bindiga 535.

Ya ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin a ranar 31 ga Yuli, yayin da yake ƙoƙarin fitar da kwantainan daga wani wurin ajiye kaya, sannan kotu ta bayar da umarnin tsare su, yayin da za a gurfanar da su a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ranar 25 ga Agusta.

Wannan kamen ya sa adadin waɗanda Kwastam ta kama kan safarar haramtattun makamai ya kai 11, yayin da adadin makaman da ta ƙwace ya kai 21,399.

Hukumar ta miƙa haramtattun makaman ga Hukumar Kula da Kuma Lalata Haramtattun Makamai ta Ƙasa (NCCSALW).

A watan Yuli 2026, Hukumar Kwastam ta miƙa wasu bindigogi ƙirar Jojef Magnum Tomahawk Shotgun guda 55, da wasu nau’o’in haramtattun makamai daban-daban guda 844, tare da kwanson harsasai 112,500, ga NCCSALW.

Waɗannan haramtattun makamai an kama su ne bayan an yi yunƙurin shigo da su Najeriya ta Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas da Tashar Jiragen Ruwa ta Onne a Jihar Ribadu, a watan Yunin shekarar 2024.

Da yake miƙa bindigogi 399 da hukumar Kwastam ta kama a Legas ga NACSALW, shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce an shigo da su Najeriya ne ranar 8 ga watan Yuli ta wani jirgin ruwa mai suna MV Velika, kuma bayan gudanar da bincike aka kama daya daga cikin mutanen da ake zargin a ranar 31bga watan, a yayin da yake ƙoƙarin fitar da kwantainar daga tashar jiragen ruwa ta Tin-Can

Ya ce an gano haramtattun makaman ne a sakamakon aiki da na’urorin binciken kayan na zamani da hukumar Kwastambta sanya da tashoshin jiragen ruwa da nufin gano kayayyaki masu haɗari da kuma daƙile ayyukan masu fasaƙwauri.

A cewarsa, Hukumar za ta ci gaba da yin iya ƙoƙarinta domin daƙile shigo da haramtattun makamai da sauran abubuwa da ke barazana ga tsaron Najeriya.

Da yake karɓar makaman, Darakta-Janar na NACSALW, Kokumo Johnson, ya bayyana cewa haramtattun makamai na taimaka wa ayyukan ta’addanci, garkuwa da mutane da tayar da ƙayar baya da kuma tashe-tashen hankula.

Ya kara da cewa daga cikin irin waɗannan makamai sama da 21,000 da aka ƙwato tun bayan kafa hukumar, zuwa yanzu ta riga ta lalata sama a guda 19,000.

Ya ce ragowar waɗanda aka kama yanzu kuma za a tattara bayanansu tare da cike sauran ƙa’idojin da suka kamata domin hana su shiga hannun miyagu.

Leave a Reply