Najeriya na kashe dala biliyan 10 kan shigo da abinci duk shekara

0 167

Ƙungiyar Sasakawa Africa Association (SAA) ta bayyana cewa Najeriya na kashe kimanin dala biliyan 10 duk shekara wajen shigo da kayayyakin abinci daga ƙasashen waje, duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na bunƙasa harkar noma a cikin gida.

Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Dokta Godwin Atser, ne ya bayyana hakan a yayin taron masu ruwa da tsaki na shekarar 2026 da kuma bikin cika shekaru 40 da kafa ƙungiyar, wanda aka gudanar a Abuja.

Ya ce daga cikin kayayyakin da ƙasar ke kashe kuɗi mai yawa wajen shigo da su akwai alkama, shinkafa, sukari, kifi da kuma tumatir da aka sarrafa.

A cewarsa, babban ƙalubalen da ke haddasa hakan shi ne ƙarancin samar da amfanin gona a cikin gida wanda bai kai biyan buƙatun al’umma ba.

Dokta Atser ya jaddada cewa akwai buƙatar samar da ingantattun fasahohi ga manoma tare da ƙarfafa ayyukan jami’an yaɗa ilimin noma domin haɓaka yawan amfanin gona.

Ya ƙara da cewa bayanai sun nuna cewa a Najeriya akwai jami’in yaɗa ilimin noma guda ɗaya ga manoma 10,000, abin da ya bayyana a matsayin babbar matsala ga ci gaban harkar noma.

Taron wanda ke ɗauke da taken “SAA @ 40: Deepening Impact and Expanding Reach at Scale”, ya mayar da hankali ne kan duba nasarorin da aka samu daga shekarar 2021 zuwa 2025 tare da tsara hanyoyin inganta noma a gaba.

Dokta Atser ya ce taron ba wai bikin cika shekaru kawai ba ne, illa wata muhimmiyar dama ce ta tattauna matsaloli, musayar ra’ayoyi da kuma tsara dabarun da za su inganta noma da samar da wadataccen abinci a ƙasar.

A nasa ɓangaren, Jakadan ƙasar Japan a Najeriya, Suzuki Hideo, ya bayyana cewa noma na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce kusan kashi 34 cikin 100 na ma’aikata na aiki a fannin, yayin da yake ba da gudunmawar kusan kashi 25 cikin 100 ga GDP na ƙasa.

Ya kuma jaddada buƙatar inganta amfani da injina a noma, rage asarar amfanin gona bayan girbi da kuma ƙarfafa kasuwannin sayar da kayayyakin noma domin ƙara yawan amfanin da ake samu.

Haka kuma, ya yabawa ƙungiyar SAA bisa rawar da take takawa tsawon shekaru 40 wajen tallafawa manoma da inganta harkar noma a Najeriya.

Leave a Reply