Shugaba Tinubu zai samu karuwar yawan kuri’u daga yankin Kudu maso Gabas a zaɓen 2027

0 639

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana kuri’un da mai girma Bola Tinubu zai samu a yankin Kudu maso Gabas.

Daniel Bwala ya ce yana da tabbacin cewa shugaban kasan zai samu karuwar yawan kuri’u daga yankin Kudu maso Gabas a zaɓen shugaban kasa na shekarar 2027.

Hadimin shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin ‘Politics Today’ na tashar Channels Tv ranar Laraba, 13 ga watan Agustan 2025.

Leave a Reply