Zan Ba Kowane Dan Amurka Dala 5,000 Idan Jam’iyyarmu Ta Samu Nasara A Zaɓe – Trump

0 43

Zan ba kowane ɗan Amurka dala 5,000 idan jam’iyyarmu ta samu nasara a zaɓe – Trump

Shugaban Trump, na Amurka ya ce zai bai wa kowane babba ɗan ƙasar dala 5,000 idan jam’iyyarsa ta Republican ta samu rinjaye a duka majalisun dokokin ƙasar a zaɓukan rabin wa’adi da za a gudanar a watan Nuwamba.

Sai dai har yanzu babu cikakken bayani kan yadda za a samar da kuɗin da kuma cewa ko hakan bai saba wa doka ba.

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron farko na jam’iyyar Republican da aka shirya domin zaɓukan tsakiyar wa’adi, inda ya yi ƙoƙarin ƙarfafa magoya bayansa gabanin zaɓukan da ake kallon suna da matuƙar muhimmanci.

Ya ce sharadi daya kawai ya ke da shi , shi ne dole ne a kashe kudin a Amurka duk da raguwar amincewar jama’a da shugabancinsa a wasu ƙuri’un jin ra’ayi, shugaban ya buƙaci mahalarta taron da su fito ƙwansu da kwarkwatarsu su kaɗa ƙuri’a, yana mai cewa su yi hakan kamar shi kansa ne ke takara a zaɓen.

Leave a Reply