Mai Mala Ya Bayyana Yadda Mayakan Boko Haram Suka Jefa Garin Geidam Cikin “Tashin Hankali”

0 134

Gwamna Buni ya bayyana cewa, halin tashin hankali da ake ciki a yankunan arewa maso gabashin Najeriya ba bakon kowa ba ne.

A cewarsa, sabbin hare-haren da suke gani a yanzu musamman lokacin da mutane ke tsaka da ibadah na da ban tsoro matuka.

Ya kara da cewa, ya zama dole a tunkare su don kawo kwanciyar hankali ga al’umman jihar Yobe.

Kalaman gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake bayyana cewa ba a ji komai daga gareshi ba tun bayan da mayakan suka farwa garin suna kashe mutane da tilastawa daruruwa tserewa.

Mutane da dama daga garin Geidam sun yi ta tserewa saboda gudun kada hare-haren mayakan Boko Haram su rutsa da su.

Al’umar yankin a cewar rahotanni, na tserewa ne zuwa karamar hukumar Yunusari da ke jihar.

Wasu hotunan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta wadanda ba a tantance gaskiyar su ba, sun nuna yadda daruruwan mutane ke tafiya kafa domin tsira da ransu.

Hakazalika an ga wasu kalilan da ke tafiya a mota sune ficewa daga yankin.

Bayanai sun yi nuni da cewa an yi artabu tsakanin mayakan da dakarun Najeriya.

Rahotanni sun ce mutane da dama sun rasa rayukansu a hare-haren ciki har da sojojin Najeriya da maharan, ko da yake rundunar sojin kasar ba ta ce uffan kan lamarin ba.

Hakazalika kokarin jin ta bakin hukumomin sojin ya cutura yayin bayanai ke nuni da cewa mayakan sun karbe garin na Geidam.

Majiyoyi daga garin Geidam sun bayyana cewa, cikin wadanda hare-haren ranar Juma’a ya rutsa da su sun hada da wata mata da ta mutu sanadin wani makamin roka da aka harba gidan surukinta, inda ta je ziyara a Geidam,

Shaidu sun ce mayakan sun kuma fasa shaguna da dama, kana suka yi awon gaba da kayan abinci mai yawa.

A baya-bayan nan dai kungiyar Boko Haram ta zafafa hare-harenta a garin Geidam da wasu garuruwan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: