Adadin masu amfani da wutar lantarki ya karu zuwa miliyan 11.71 a shekarar 2023

0 98

Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, ta ce adadin masu amfani da wutar lantarki ya karu da mutum 240,000 daga miliyan 11.47 a zango na biyu na shekarar 2023 zuwa miliyan 11.71 a zango na uku na shekarar 2023.

Hukumar NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na na zango na uku na shekarar 2023 da aka fitar a Abuja a yau Alhamis, inda ta ce karin ya kai kashi 2.08 cikin dari.

Manema labarai sun bayyana cewa rahoton ya mayar da hankali kan lissafin kudaden shiga da aka samu, da kuma na abokan ciniki na kamfanonin rarrabawa wutar lantarki.

Rahoton ya bayyana cewa a kowace shekara adadin masu amfani da wutar lantarki yakan karu da kashi 7.09 a cikin zango na uku 2023 daga miliyan 10.94 da aka ruwaito a cikin zango na uku a shekarar 2022. A cewar hukumar NBS, zangon karshe na 2023, yawan masu amfani da tsarin mita sun kai miliyan 5.68 daga miliyan 5.47 da aka tantance a cikin zango na biyu na shekarar 2023, wanda ke nuna karuwar kashi 3.77 cikin dari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: