Aisha Iliyasu ce halastacciyar shugabar Ƙungiyar ‘Yan Jaridu Mata ta Kasa a Jihar Jigawa – NAWOJ

0 334

Kungiyar ‘Yan Jaridu Mata ta Kasa, NAWOJ ta jaddada Aisha Iliyasu Abubakar da aka zaba ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin halastacciyar shugabar kungiyar a jihar Jigawa.

Kungiyar ta kuma yi watsi da zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Nuwamba, 2023, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ya saba ka’idoji da tanade-tanaden dokokin gudanar da Kungiyar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a takardar da ta raba wa manema labarai jiya, wadda ke dauke da sa hannun Sakatariyar Kungiyar ta kasa, Helen Udofa.

Takaddar ta tabbatar da sahihancin zaben ranar 1 ga watan Nuwamba wanda aka zabi Aisha Iliyasu Abubakar a matsayin shugabar kungiyar, da Bushira Muhammad mataimakiya, sai kuma Salamatu Nuhu a matsayin Sakatariya da Maryam Ibrahim mataimakiyar Sakatariya, da Aisha M. Sani mai rike da mukamin Ma’aji.

Kungiyar ta kuma gargadi wadanda suke ikirarin cewa sune shugabin da cewar su guji sabawa kai’idojin kungiyar, sannan ta yi kira ga hukumomi da sauran kungiyoyi da su guji yin dukkan wata mu’amalla da wadanda ke ikirarin shugabancin ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: