Akalla mutane 123,000 ne suke gudun hijira a zirin Gaza

0 208

Sama da mutane dubu 123 ne suka kauracewa gidajensu a zirin Gaza tun bayan barkewar sabon rikici tsakanin bangarorin kasashen Palastine da isra’ila.

A cewar majalisar dinkin duniya, sama da mutane dubu 73 sun fake a makarantu, inda aka mai dashi sansanin yan gudun hijira.

Isra’ila ta kaddamar da harin sama da daruruwan jirage marasa matukai a Gaza a ranar Asabat, lokacin da Hamas ta kaddamar da mummunan hari kan Isra’ila tare da tarwatsa dubban makaman roka a kasar.

Kakakin cibiyar majalisar dinkin duniya dake sansanin falasdinawa Adnan Abu Hasna yace adadin yan gudun hijrar ka iya zarce haka. Gaza dake zama matsugunin falasdinawa akalla miliyan 2.3, wadanda ke rayuwa karkashin matsi da tashin hankalin Isra’ila bayan Hamas ta kwace iko a 2007.

Leave a Reply

%d bloggers like this: