Akalla mutum dubu 3 da 125 wandada basu ji basu gani ba aka kashe yayin da akayi Garkuwa da mutane dubu 2,703 cikin watanni 11

0 124

Akalla mutane dubu 3 da 125 wandada basu ji basu gani ba aka kashe, yayin da akayi Garkuwa da mutane dubu 2,703 cikin watanni 11 da suka gabata a arewacin kasar nan a cewar jaridar Punch.

Jaridar ta gano hakan ne cikin rahotanni da jami’an tsaron kasar nan suke fitarwa da cibiyar kididdiga ta kasar Amurka da kuma rahotannin Da gwamnatin jihar kaduna take fitar wa, daga watan janairu zuwa satumba na wannan shekarar.

Wannan na zuwa jim kadan bayan wasu daga cikin mayan arewacin kasar nan, wandanda suka hada da shugaban kungiyyar cigaban yankin Jihohin tsakiyar kasar nan DR. Pogu bitrus da kuma mataimakin shugaban kungiyyar kiristoci ta kasa Joseph Hayab suke korafi akan yanda ake cigaba da kashe mutane a fadin kasar nan.

A cikin rahotan Punch ta gano cewa, mafi akasarin wadanda suka mutu sunfito ne daga Jihohin Kaduna, Zamfara, Sokoto, Katsina, Niger and Borno.

Haka zalika kididdigar da gwamnatin jihar kaduna take fitarwa, ta gano cewa a jihar kaduna an kashe mutane 888 da kuma yin Garkuwa da mutane dubu 2 da 553 daga watan Janairu zuwa Satumba na 2021.

Leave a Reply

%d bloggers like this: