Alhaji Attahiru Bafarawa ya jaddada takaicinsa inda yace shugaba Buhari ya ji tsoron haɗuwarsa da Allah

0 256

Tsohon gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya bayyana takaicinsa kan kashe-kashen al’umma da ‘yan bindiga ke yi a yankin, yana mai kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya ji tsoron haɗuwarsa da Allah.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata hira da sashen hausa BBC biyo bayan ‘yan fashin dajin da suka ƙona wata motar bas ɗauke da mutum kusan mutum 30 a cikinta Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Sokoto.

Hare-haren na masu garkuwa da mutane na ci gaba da haddasa salwantar rayukan al’umma a yankin arewa maso yammacin kasar nan.

Lamarin ya fi ƙamari a ‘yan kwanakin nan a yankin Isa da Sabon Birni na jihar Sokoto da kuma yankin Shinkafi a jihar Zamfara duk da kokarin da gwamnatin tarraya da na jihohin ke cewa suna yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: