An amince da takardar neman sayen karin kayan abinci domin ciyarwar buda baki a jihar Jigawa

0 102

A daidai lokacin da gwamnatin jihar Jigawa ta kuduri aniyar rage wahalhalun da al’ummar jihar nan ke fuskanta sakamakon karin farashin kayan abinci, majalisar zartaswar jiha ta amince da takardar da ma’aikatar ayyuka ta musamman ta gabatar a gaban majalisar don sayen karin kayan abinci domin buda baki a wannan watan na Ramadan.

Majalisar ta amince da zunzurutun kudi har biliyan biyu da miliyan dari takwas da talatin da biyar da miliyan dari uku da ashirin da daya, domin ciyar da al’umma a wanann watan.

Majalisar dai a zamanta ta amince da samarda cibiyoyi 609 na ciyarwa a fadin jihar tare da mafi karancin cibiyoyi guda 2 a unguwanni 287 domin rabon abincin buda baki musamman ga talakawa da marasa galihu. Hakazalika, Majalisar ta aminta da kafa cibiyoyin buda baki a Manyan Makarantu guda 10 da ke Jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: