An kama wasu mutane 7 da ake zargi da hannu a satar ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Wukari

0 112

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Taraba, David lloyanomon ya bayyana cewa an kama wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a satar ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Wukari.

Kwamishinan ya ce an kama mutanen da ake zargin ne a cikin daji.

Ya ce, ana sa ran binciken da aka fara zai bankaɗo wurin da aka ɓoye ɗaliban da aka sace.

Jami’ar hulda da jama’a na Jami’ar Mrs Adore Awudu ta ce Joshua Sardauna daga sashin tattalin arziki da kuma Obianu Elizabeth Chiwuadu daga sashen nazarin halittu ne ɗaliban da aka sace. Rahotanni sun ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace ɗaliban biyu na Jami’ar Tarayya ta Wukari da ke Jihar Taraba

Leave a Reply

%d bloggers like this: