An kama yan fashi da makami guda 5 a jihar Jigawa

0 410

Rundunar yan sandar jihar jigawa ta kama yan fashi da makami 5 a wurare daban-daban a jihar, tare da kwace muggan kwayoyi a hannun su.

Cikin wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar DSP Lawan shisu Adam yace daya daga cikin mutanan mai suna Ashiru Musa dan shekaru 24 dan asalin kyauyen Kyaran dake karamar Hukumar Dutse,yayiwa wani mutum barazana da wuka inda ya kwace masa Babur. Sanarwar tace wanda ake zargin ya amsa laifin sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: