An rufe iyakoki kuma an hana zirga-zirga a yankunan dake makwabtaka da Nijar

0 311

Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa, ta ce biyo bayan halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar, ta tura jami’ai domin duba duk hanyoyin da bakin haure za su iya shigowa ta cikin su.

Kwanturolan hukumar mai kula da Jibiya a jihar Katsina Mustapha Sani, shi ne ya bayyana hakan a wani bikin hadin gwiwa da rundunar ‘yan sandan jihar domin bikin cika shekaru 60 da kafuwar hukumar.

A cewarsa, da halin da ake ciki yanzu an rufe iyakokin kuma an hana zirga-zirga a yankunan.

Don haka ya shawarci ‘yan Najeriya da ke shirin tafiya Nijar da su zauna a gida, yana mai cewa ‘yan Najeriya da ke komawa gida ne kawai aka ba su damar shigowa.

Yayin da yake jawabi ga jami’an hukumar da kuma jami’an rundunar, Sani ya ce an mayar da tsarin hukumar zuwa ta zamani da fasfo wanda yake cikin mafi inganci a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: