Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce majalisar ta yi karba tare da yin muhawara kan kudurori 2,263 tun bayan kafuwar majalisar ta goma cikin shekaru biyu.
Ya bayyana hakan ne a zaman hadin gwiwa na musamman da aka gudanar tare da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar dimokuradiyya domin tunawa da cikar shekaru biyu da fara aiki na majalisar.
Tajudeen ya ce majalisar ta bullo da shirin aiki na bangarori takwas da suka yi daidai da ajandar “Sabon Fata” na shugaban kasa, inda ya ce hakan ya haifar da ci gaba a fannoni da dama.
Ya kara da cewa majalisar ta ware Naira tiriliyan 6.11 ga harkar tsaro a kasafin shekarar 2025, yayin da sabbin dokoki kan masana’antar kera makamai da sarrafa makamai kanana suka kara karfafa ikon gwamnati.