Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta tabbatar da nasarar jigilar fiye da Alhazai dubu 14,000 daga Saudiyya zuwa Najeriya a ci gaba da gudanar da aikin hajjin bana na 2025.
Cibiyar sa ido da umarni ta NAHCON da ke Makkah ta bayyana cewa jirage biyu na Flynas sun tashi daga Jeddah zuwa Sokoto da Abuja, inda suka ɗauko Alhazai 847 da jami’an lura 8.
Hakan ya kawo adadin jiragen da aka kammala zuwa 33, yayin da aka ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomi da kamfanonin jiragen sama domin tabbatar da zaman lafiya da sauƙin tafiya.
NAHCON ta ce tana ci gaba da sa ido daga cibiyarta a Makkah domin ganin duka Alhazai sun samu damar yin ibadarsu ba tare da wata matsala ba.