Ana sa ran titin layin dogo daga Kano zuwa Maradi zuwa shekarar 2025

0 298

Ana sa ran kammala aikin titin layin dogo daga Kano zuwa Maradi na Jamhuriyar Nijar da zai lakume dala biliyan biyu da gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kaddamar, ana sa ran kammala aikin zuwa shekarar 2025.

Da yake jawabi yayin wata ziyarar aiki da yaki wajen aikin da ya faro daga Dawanau a Kano zuwa Jamhuriyar Nijar, Ministan Sufuri, Sanata Saidu Ahmad Alkali, ya bayyana jin dadin yadda ayyukan ke gudana.

Ya ce, aikin shimfida fandisho ya kai matakin kammala da kashi 80 cikin 100, kuma za a fara aikin layin dogo na hakika nan ba da dadewa ba.

Dangane da ko dan kwangilar zai cimma burin kammala aikin cikin lokacin daya ambata, ministan ya nuna gamsuwa da kwarin guiwa da yadda aikin ke gudana.

Saidu Alkali ya kuma ya yaba aikin share daji, kuma kwangilar tana tafiya yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba. Kazalika, Ministan ya ce akwai bukatar dan kwangilar ya kasance a shirye domin sadaukarwa ga ci gaban kasa a karkashin jagorancin gwamnatin Tinubu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: