Atiku Abubakar ya rasa mukamin sa na gargajiya na Wazirin Adamawa

0 176

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya rasa mukamin gargajiya na *Wazirin Adamawa*, bayan da gwamnatin jihar ta fitar da sabon umarni da ke tilasta a cire duk masu rike da mukamai a majalisun gargajiya da ba ‘yan asalin yankin su ba.

Atiku ya karɓi sarautar Wazirin Adamawa daga Lamidon Adamawa Muhammadu Barkindo a shekarar 2018, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan majalisar masarautar Adamawa.

Sai dai wata wasika da ma’aikatar kula da harkokin masarautu ta fitar ranar 19 ga watan Yuni, mai ɗauke da sa hannun babban sakatare Adama Felicity Mamman, ta umarci a sallami duk waɗanda ba ‘yan asalin yankunan da suke wakilta ba daga matsayin su na masu zaben sarakuna da ‘yan majalisa. Wasikar ta bayyana cewa waɗanda kawai aka ba sarauta ba tare da mukamin majalisa ba, za su iya ci gaba da zama, amma sauran su, ciki har da Atiku, da ba yan asalin yankin masarautar Adamawa, sun rasa matsayin su.

Leave a Reply