Fiye da mutum goma sun rasu a hatsarin mota a babban hanyar Lagos – Ibadan da ke jihar Oyo

0 114

Fiye da mutane goma ne ake tsoron sun mutu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a safiyar yau Talata a kan babbar hanyar Lagos-Ibadan da ke jihar Oyo.

Haɗarin ya haɗa da motocin haya na Nissan Micra guda uku da manyan motocin ɗaukar kaya guda uku, dukkansu na barin unguwar Iwo Road ne kafin hatsarin ya auku.

Hukumomi da masu aikin ceto sun shiga aikin fidda gawarwakin a cikin laka.

Wannan lamari ya sake jefa tambaya kan rashin ingancin hanyoyin tafiye-tafiye a fadin kasar nan.

Leave a Reply