Mai Alfarma Sarkin Musulmai Kuma Shugaban Jama’atul Nasril Islam, Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad, yace babu taron lakca, wa’azi da tafsirin Ramadan a wannan shekara, saboda barkewar annobar corona.

Sarkin ya kuma ayyana cewa babu sallar jam’i a masallatai dake fadin kasarnan a wannan shekarar.

A wata sanarwa wacce sakataren Jama’atul Nasril Islam, Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya fitar, Sarkin Musulman ya bukaci dukkan musulmai da suyi sallolinsu a gida, kasancewar baza su laminci ganganci da rayuwarsu ba.

Sarkin ya hori musulmai da su karanta Al-Qur’ani mai tsarki tare da sauraron lakcocin, wa’azozi da tafsiran watan Ramadan ta shafukan intanet da sauran hanyoyi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: