Dakatar da Betta Edu zai sa kowa ya shiga taitayin sa – Shekarau

0 226

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yaba wa Shugaba Tinubu kan matakin dakatar da Ministar Ma’aikatar Jin Ƙai, Betta Edu domin ba hukumar EFCC damar gudanar da bincike kanta bayan zargin hannu a badaƙalar kuɗaɗe.

Shekarau ya kuma ce “a baya ana yawan samun zarge-zargen cin hanci da rashawa a ƙasar amma ba a ɗaukar mataki”, bisa hakan ne matakin shugaban ya burge shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: