Dalilan da yasa shugaba Buhari yaƙi saka hannu akan sabuwar dokar zaɓe

0 200

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rubuta wasika zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, yana bayyana dalilansa na kin rattaba hannu akan kudirin dokar zabe na bana.

Shugaban kasar, cikin wasikar, yace abubuwan da suke faruwa a kasarnan baza su bar shi ya sanya hannu akan kudirin ba.

Shugaba Buhari ya ambaci tsadar gudanar da zaben cikin gida, da kalubalen tsaro wajen sanya ido a zaben, da cin zarafin hakkokin ‘yan kasa da wariyar da ake nunawa kananan jam’iyyun siyasa, a matsayin dalilan da suka sanya shi kin amincewa da kudirin.

Shugaban kasar ya kuma ce ya samu shawarwari daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati dake da alaka, kuma ya bibiyi kudirin a tsanake bisa la’akari da abubuwan dake wakana a kasarnan.

Shugaban kasar yace zai fi dacewa a kyale kowace jam’iyyar siyasa ta yanke shawarar yadda zata gudanar da zabenta na cikin gida.

Kwanaki 30 da aka bawa Shugaba Buhari na ya sanya hannu akan kudirin sun kare a ranar Lahadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: