Ecowas ta bayyana damuwarta kan ɗage zaɓen shugaban ƙasar Senegal

0 246

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta bayyana damuwarta kan matakin da hukumomin ƙasar Senegal suka ɗauka na ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka shirya gudanarwa ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Shugaban ƙasar, Mackey Sall ya danganta dalilin ɗage zaɓen da rikicin siyasa da ya kunno kai a ƙasar, wanda kuma ya sa aka hana da dama daga cikin ‘yan takarar tsayawa zaɓen.

Cikin wata sanarwar da Ecowas ta fitar a daren ranar Asabar, tayi kira ga hukumomin Senegal da su bi hanyoyin da suka dace, tare da sanya sabuwar ranar zaɓen.

Ecowas ɗin ta kuma umarci ‘yan siyasar ƙasar da su haɗa hannu, wajen tabbatar da gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a ƙasar.

Sanarwar ɗage zaɓen da shugaba Sall ya yi, ta jefa al’ummar ƙasar cikin halin rashin tabbas, inda ‘yan adawa ke kallon matakin a matsayin tauye kundin tsarin mulki. Wannan dai shine karon farko da aka taba dage zabe a Senegal. Kasar ta kuma gudanar da sauyin shugabancin farar hula cikin lumana har sau huɗu tun bayan da ta samu ‘yancin kai daga ƙasar Faransa a shekarar 1960.

Leave a Reply

%d bloggers like this: