Ficewar Atiku daga PDP ba sabon abu ba ne, muna tsammanin dawowarsa in ji Damagum

0 400

Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP, Umar Damagum, ya bayyana cewa ficewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, daga PDP ba sabon abu ba ne a tarihi. A cewarsa, hakan ya taba faruwa a baya kuma sun yi tsammanin hakan na iya sake faruwa.

Damagum ya ce:

“Wannan ba karo na farko bane da Atiku ke barin jam’iyyar. A siyasance, mutane sukan sauya sheka saboda dalilai daban-daban, kuma ba abin mamaki bane idan ya dawo kamar yadda ya saba.”

Ya kara da cewa jam’iyyar PDP ba za ta tsaya akan mutum guda ba, domin tsarin jam’iyyar na tafiya da mutane masu kishin kasa da tsarin dimokuradiyya.

Wannan na zuwa ne bayan rahoton ficewar Atiku daga jam’iyyar, wanda ya janyo ce-ce-ku-ce daga magoya baya da masu sharhi kan siyasa a Najeriya.

Leave a Reply