Gwamnatin Jigawa tana shirin kafa wani ƙaramin kamfani na ƙera magunguna

0 882

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce tana shirin kafa wani ƙaramin kamfani na ƙera magunguna domin ƙara sauƙaƙa samun ingantattun magunguna tare da rage dogaro da masu samar da su daga waje.

Babban Manajan Kamfanin Magunguna na Jihar, JIPHARMA, Nasiru Alhassan, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a birnin Dutse, yayin da yake nazarin ayyukan kamfanin cikin shekaru biyu na mulkin Gwamna Umar Namadi.

Ya ce an riga an tanadi fili a layin masana’antu na Gagarawa domin gina masana’antar da za ta fara samar da muhimman magunguna kamar Vitamin C, paracetamol da syrup, wanda hakan ke nuna babbar nasara a fannin kiwon lafiya na jihar.

Leave a Reply