Tallafin wutar lantarki da gwamnati ke bayarwa ya tashi daga biliyan 610 zuwa tiriliyan 1.94 daga shekarar 2023 zuwa 2024
Tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa ga bangaren wutar lantarki a Najeriya ya haura kashi 219 cikin ɗari, inda ya tashi daga naira biliyan 610 a shekarar 2023 zuwa naira tiriliyan 1.94 a shekarar 2024, kamar yadda rahoton jaridar The PUNCH ya nuna.
Hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta ƙasa, wato NERC, ta danganta wannan hauhawa da cire tallafin man fetur, karya darajar naira a watan Yuni na 2024, da kuma daskarar da farashin wutar lantarki tun daga shekarar 2022 duk da hauhawar farashin kayayyaki da kuɗin samar da wuta.
Duk da cewa buƙatar sanya tallafi ta kai tiriliyan 1.94, gwamnati ta biya naira miliyan 371 kacal zuwa yanzu — wanda bai kai ko kashi ɗaya cikin ɗari na buƙatar ba — lamarin da ke ƙara tayar da hankali game da dorewar harkar wutar lantarki.
Rahoton NERC ya ce sabbin dokokin da ke tilasta kamfanonin rarraba wuta su biya dukkan kuɗin da ake bin su, na da nufin hana matsalolin bashi na tallafi daga tabarbarewar tattalin arzikin sashen wutar lantarki.