Fitar da kayayyakin amfanin gona daga Najeriya zuwa wasu kasashe ya karu da kasho 123 – NBS

0 90

Sabbin bayanai da Hukumar Kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar, sun nuna cewa fitar da kayayyakin amfanin gona daga Najeriya zuwa wasu kasashe, ya karu da kashi 123,  bisa kimar da aka samu a rubu’i na hudu na shekarar 2023 na (₦463.97bn), da kuma kashi 270  idan aka kwatanta da ƙimar da aka rubuta a Q1, 2023 (₦ 279.64 biliyan).

Rahoton da NBS ta fitar kan ‘Kasuwar Kayayyaki’ na Q1, 2024, ya nuna cewa yawancin kayayyakin noman ana fitar da su ne zuwa nahiyar Asiya, wanda darajarsu ta kai billiyon ₦572, sannan aka fitar da su zuwa Turai da ₦366bn.

A daya bangaren kuma, jimillar shigo da kayayyakin noma a Q1, 2024 ya kai naira billiyan dari ₦920bn daidai da kashi 7.28 na jimillar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje.

Ansamu karuwa da kashi 29.45 idan aka kwatanta da darajar  Q4, 2023 naira billiyan dari 7. 11 daidai kenan da kashi 95 idan aka kwatanta da darajar da aka rubuta a Q1, 2023 na naira billiyan dari 471bn.

Leave a Reply

%d bloggers like this: