Fulbe political awareness ta zabi sabbin shugabanni da zasu ja ragamar kungiyar a jihar Jigawa

0 141

Sabuwar Kungiyar siyasa ta Fulbe political awareness continuity for Danmodi 2027 ta zabi sabbin shugabanni da zasu ja ragamar kungiyar a jihar Jigawa.

Wadanda aka zaba sun hadar da Saidu Musa Gagarawa shugaba da Musa Adamu sakatare da Wada Wurma Ma’aji da Sani Rimi mataimakin shugaba da Usman Abdullahi mataimakin sakatare da Ado Baso shugaban matasa da Mati Jana kakakin kungiya da Idi Ruwa sakataren tsare tsare da Hindo Nagawu Hardon Hausawa.

Haka kuma kungiyar ta nada Honourable Ibrahim Garba Hannun Giwa da Sanata Mustapha Kiyawa da Aminu AK Babura da Muhammad Alhassan da kuma Dr Abdullahi Dogo Abubakar a matsayin Iyayen kungiya.

Shugaban kungiyar Sa’idu Musa Gagarawa, ya ce an kafa kungiyar ne domin wayar da kan Fulani bukatar ganin Gwamna Umar Namadi ya yi tazarce a zaben 2027.

Leave a Reply